Disneyland 1972 Love the old s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin

Sayyed Zakzaky2

Ina hukuncin bi ta gaban mutum idan yana salla?
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, na ji ana cewa idan an gayyaci mutum walima zai iya ya ci abincin ko da yana azumi. Shin haka ne?

Daga Ahmad Abdullah da Usman Ridwan

SHAIKH ZAKZAKY: Haka ne, amma da dan bambanci. Ba a ce, idan an gayyace ka walima wanda yake kana cikin mutane da yawan gaske, kamar walimar biki, bai zama wajibi ka ci ba, kana iya cewa kana azumi, saboda dama abincin ba domin kai daya aka yi ba. An yi don mutane da yawa ne, kai kuma daya daga cikinsu ne. Saboda haka rashin cin ka ba zai cutar da mai yin abincin ba.

To amma idan ka gaya wa wani za ka ziyarce shi lokaci kaza, kana nan zuwa da karfe 2: 00 na rana, misali. To sai ka zo, sai ya kawo abinci, to wannan ne ya zama 'lazim' ka ci, saboda ya shirya domin ka ne 'khasatan.' Kuma idan har ba ka ci ba, to lalle ka cutar masa, ya yi tanadi musamman domin ka, kuma ga shi ka ki ci. Ba za ka ce masa kana azumi ba. Shi ne ko dai da yake kana azumin sai ka ci, kana da ladan azuminka. Amma za ka takaita ga wannan cin ne kawai, ka ci daidai gwargwado ba wani ci matsananci ba. Sannan kuma akalla dai ka ci abincin nasa, shi kenan, kuma daga nan sai ka ci gaba da azumin naka, kuma kana da ladan azumin. Ta wannan fuskar ne kawai ya zama wajibinka ne ma ka ci. Amma ba duk walimar buki da aka gayyace ka ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ina kallon labarai kuma mai yin labaran ba ta sa hijabi. Shin ya halasta in ci gaba da kallon labaran?

Daga Sulaiman Abbati Tela Alkaleri Bauci

SHAIKH ZAKZKY: Eh haka ne ya halatta, idan misali kallon labarin ne kawai hadafinka, amma a dinga kura mata ido har ka sawwala wani abu a ranka, to ta nan ya haramta, wannan kuwa ko da ta sa hijabi. Wato akwai kallo da ake ce masa 'RIBATAN,' wanda shi haramun ne, ba hijabi ko da hijabi, da rashin hijabi ya fi zama 'ribatan' ya fi shigowa. Sai mu ce ba hijabi ko da hijabi, kallo 'ribatan' ya haramta. Amma in kallon labari ne kawai a yayin da take karanta labarin, to babu laifi. Kodayake akwai wadansu ba'adin Malamai da suke cewa, idan ya zama 'mubashir' (kai tsaye) ya fi tsanani. Idan wato ya zama kai tsaye ne take magana din, ina ganin kauce wa kallon shi ya fi.

Ala'ayyi halin dai, idan mutum ya ga irin shigar mai karanta labarin ya zama wani iri, akwai dibaru da mukan yi a talabijin. Ban san ba ko kowane talabijin na da wannan ba. Talabijin din da nake da shi dai yana da 'text,' (rubutu), idan na matsa sai ya rufe mani hoton sai sauti. Har ila yau, a 'reciever', wani yana da 'blue' kala ne. Wani 'reciever' zai yiwu yana da 'blue', in ka matsa 'blue', sai ya rufe hoton, sai ka ji sauti. Saboda haka in na ga abin da ba na bukatar na kalla, nakan matsa wannan ne, sai ya zama sai in ji sauti din. In na tabbatar ana nuna abin da ya shafi labaran ne, sai in bude. In an dawo, sai in sake matsa 'blue' din. Saboda haka tunda wasu suna yin wata irin shiga wadda shigar dama kamar sun yi ta ne don su yi tabarruji, masalan, to irin wannan rashin kallon shi ne mafi a'ala.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, yaya matsayin tuban wanda ya yi karya, amma bai yi azumi uku ba kamar yadda ake yi?

Daga Abdulkarim Tudun Wada Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To lalle mai yiwuwa yana nufin wanda ya yi rantsuwa ne bai yi kaffara ba, domin rantsuwa ce ake mata kaffara. In mutum ya yi rantsuwa ya karya rantsuwar, zai yi kaffara. Amma ba a ce in mutum ya yi karya, sai ya yi azumin kwana uku ba. Idan mutum ya yi karya kam ya yi haramun, amma ba a ce yana yin kaffara da azumin kwana uku bane. Saboda haka wanda ya yi ratsuwa, ya karya rantsuwar, ko ya yi alwashi ga Allah, ya zama bai cika alwashin nasa ba, to kaffara ta hau kansa, kuma kaffaran nan ba ta faduwa, tana nan a kansa har ya mutu. Kuma ko bayan ya mutu, ana bin sa bashi, saboda haka har magadansa zai hau. Saboda haka, ka ga ba ta faduwa kenan.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ina hukuncin bi ta gaban mutum idan yana salla?

Daga Shehu Kani Jimeta Yola.

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle ba a ruwaito wani hukunci dangane da wannan ba. Saboda haka ratsa salla, sai dai in ana ganin sa ta fuskacin rashin girmamawa ne ga sallar, amma in ba haka ba, lalle bai shafi sallar ba. Tunda cikin ruwayoyi ya nuna har mutum ma a kan jaki yakan zo ya ratsa ya wuce kuma ana salla. Har jaki ma yakan ratsa salla, kuma salla ta yi. Amma abin da 'amah' take ruwaitowa cewa idan mutum ya zo zai ratsa sallarka ka tunkude shi, in ya ki ka yake shi domin Shaidan ne, wannan bai inganta ba. Kuma ba za a taba yin hukunci da shi ba. Kuma ma bisa gaskiya ma ya saba hankali da basira. Da kuma ruwayar da har ila yau 'amah' take kawowa cewa, mace da jaki da bakin kare suna bata salla, shi ma wannan kagaggen hadisi ne, kuma ma ya saba hankali da basira. Don mutum ya ratsa ta gaban sallarka, bai shafi sallarka da komai ba, sallarka kuma na nan, ba abin da ya shafe ta. Kuma ba ruwanka da mai wucewa ta gabanka, saboda sallar tafiya take ruhiyyan ya zuwa ga Allah (T). Ba jiki ne ba, ballantana wani jiki da ke motsi ya tunkude ta ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ni dan kasuwa ne kuma jama'a suna ba ni ajiyar kudi, sai dai ba su gaya mini lokacin da za su zo su amsa. Shin zan iya daukar wannan kudaden ajiyar in sa su a cikin harkokin kasuwancina tunda duk lokacin da suka zo nema ina ba su ba wata matsala?

Daga Abdurrashid Abubakar Abuja.

SHAIKH ZAKZAKY: To wannan shi ne ma dalilin da ya sa suka ba ka ajiyar, dama ba suna sa tsammanin za ka bude tukunya ne ka zuba masu kudinsu, in sun zo ka dauko ka ba su ba. Suna ganin tunda kai dan kasuwa ne, ko da wane lokaci kana jujjuya kudi, duk lokacin da suka zo neman kudinsu za su sami abinsu, shi ya sa suka aminta suka ba ka wannan ajiya din. Kuma da wannan fahimtar ne ma dai suka ba ka din. 'Allahumma' sai dai idan wani ya kawo kudin nasa ya ce amma wannan kar ka taba, sami wani akwati ka kulle, sai na zo ka bude ka ba ni. Sai dai in haka suka yi. Amma in dai matukar ya ba ka kudi ne, ya zo kuma wani lokaci ya ce ka ba shi kudin, ka ba shi kudin, kuma ya yi daidai, to ba laifi don ka yi amfani da shi. Amma da za a ce mutum wani hakkinsa ya fado hannunka, misali kamar kudinsa ne ya zo hannunka ta wani dalili, sai ka dauka ba da izininsa ba, ka yi ciniki da shi. To in ka ci riba, ribar har da shi. Sai ka fid da naka dawainiyar ka hada masa da ribarsa. In kuma ka fadi, faduwarka ce, ba za a raba faduwar da shi ba, tunda dama bai ba ka ba. Saboda haka in aka sami faduwa, kai za ka cika masa. In kuma an sami riba, yana da kaso a riba din. Wato kenan wanda yake ba da izininsa ba kenan ka dauka ka yi. Amma wannan, kamar yadda yake fadi a fahimtata, da ma su ma sun ba da kudin, ba suna tsammanin zai ajiye bane, sun aminta ne ya juya din, kuma ba suna bukatar ya ba su wani abu daga cikin ribar bane, tunda dai sun sami garanti, duk lokacin da suke bukatar kudinsu za su samu.

TAMBAYA: Assalamun alaikum. Allah ya ji kan Malam, idan zama ya hada ni da wanda ba Musulmi ba a daki daya (a zaman makaranta), to ga shi Musulunci ya ce kafiri najasa ne. To Malam ko ya halasta idan ya dafa abinci ya kira ni mu ci, in ci abincin tare da shi, sannan ni idan na dafa nawa abincin ya halasta in kira shi mu ci tare? Saboda Malam ina hangen in har ya kira ni mu ci abincin na kiya, ko na ki kiran sa ga nawa abincin, zai ga kamar ina kyamar sa. Ko wannan kyamar tana iya zama a matsayin cutawa gare shi? Sannan Malam yaya ya kamata in yi mu'amala da wanda ba Musulmi ba ta yadda zan iya nuna masa hikima da karimci na Musulunci? halastakabirmaradun2001@yahoo.co.uk

SHAIKH ZAKZAKY: Batun najastuwar kafiri, haka din ne. Saboda haka ka ga idan abincin da za su ci tare ya zama irin wanda ake dangwala hannuwa ne, kamar yadda ake ajiye tuwo a yago shi a tsoma shi a miya, to lalle 'lazim' a kyamaci wannan. Amma in zai yiwu abinci wanda ka aminta lafiya lau ne, kamar yadda za a ajiye, kowa ya diba a nasa farantin, wannan babu laifi da shi. Amma shi ma sai ka aminta da tsarkin abincin, ya zama ba wanda kuka cakuda hannuwa ne ba, ballantana ka ji kyamar jibinsa. Sannan kuma daidai gwargwado, tare da kana kyamarsa shi najasa ne, ka yi hikimar da yake a lokacin kuma, a matsayinka na Musulmi, kana kallon sa a matsayinsa na mutum ne, sai ka yi masa bayanin da zai iya ganewa cewa mu a Musulunci akwai abubuwan da muka dauka ba su da tsarki, mukan ce masa najasa, wanda suka hada da bayan gida da fitsari da mushe da wadansu abubuwa irin wadannan wanda ba mu mu'amala da su. Da giya da naman alade da ire-iren wadannan, wadanda suke tunda mun dauka najasa ne ba mu ta'ammuli da su. Saboda haka, lalle a zamanku dole ya kiyaye, ya nisanci wadannan najasu. Kuma ya san cewa in ma bai nisanta ba, in ya yi hulda da su, kai dole za ka ja baya a yayin da kake hulda da shi, saboda ya san cewa kai ka dauki wadannan abubuwa kazanta ne, kuma ba ka ta'ammuli da su. In ma misali ya mika maka hannu kuma kana ganin hannun akwai najasa, kuma in ka yi masa bayanin cewa saboda kaza ba zai yiwu in yi wannan ba, ko kuma in hannu ne kana iya karba ka wanke. Amma kamar abinci kana iya gaya masa cewa ba zai yiwu ba. Daidai gwargwadon yadda yake iyawa.

Na san irin wannan zaman ya hada ni da wadanda suke ba musulmi ba a kurkuku, kuma sukan kawo abinci. Nakan ci, amma ba muna hada hannu muna daddangwalawa bane, ana diba ne. Kuma wani lokaci sukan kawo in yi musu bayanin cewa wannan ba zai yiwu in ci ba. An taba kawo min ma dodon kodi, na ce na gode. Suka ce lalle wasu na kyamar dodon kodi, na ce haka ne, a bisa gaskiya ba dai na ci. Wata rana aka kawo naman kaza na tambaye su yaya aka yanka? Ya ce shi ma bai sani ba, na ce ba zai yiwu in ci ba. Amma abincin da suke saya na kasuwa kamar naman saniya yakan kasance dama yankan musulmi ne, don haka ba tsoro dangane da wannan. Na san har sukan yaba suna cewa ga shi muna tare ba a kyamar su. Kuma ya kawo musu fahimtar addininmu ba yadda suka dauka bane. Amma dai dole ka yi musu bayanin cewa kai a wurinka akwai wasu abubuwa da suke ba masu tsarki bane.

TAMBAYA: Allah ya ji kan Malam, menene hukuncin sayen abinci wanda ake tu'ammali da hannuwa a wajen hada shi (kamar kosai, da shinkafa) a wurin kafiri, shin ko ya halasta? halastakabirmaradun2001@yahoo.co.uk

SHAIKH ZAKZAKY: Idan hannunsa na taba kuma ba a aminta ba da tsarkin hannunsa da cakudar jibinsa, to dole a nisanta. Amma idan mai karbar wankewa ne, ana iya karba daga gare shi a wanke. In kuma ba mai karbar wankewa bane, ya cakuda da shi ne, to sai a nisanci wannan.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din